Sharhi:Manufar Sarkin Saudiya Na Gayyatar Shugabani 17 Zuwa Birnin Riyad
Sarkin Saudiya Salman bn Abdul-Aziz ya tura goron gayyana ga Shugabanin kasashen musulmi 17 domin su gana da Shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Riyad.
A karshen wannan wata na Mayu da muke ciki ne ake sa ran Shugaban kasar Amurka Donal Trump zai kai ziyara zuwa birnin Riyad na kasar Saudiya, a ranar 10 ga watan Mayu, Ma'aikatar harakokin wajen Saudiya ta sanar da tura wasikun gayyata ga Shugabanin kasashe 17 na kasashen musulmi zuwa birnin Riyad a daidai lokacin da Shugaba Trump zai ziyarci kasar ta Saudiya daga cikin wadanda aka gayyata akwai Khalifa bn Zayid Ali Nahyan sarkin hadaddiyar daular Larabawa, Hamad bn Isa Ali Khalifa Sarkin kasar Bahrain, Tamim bn Hamad bn Khalifa Ali Sani,sarkin kasar Qatar, Sabah Ahmad Jabir Sabah sarkin kasar Kuweit, da Recep Tayyip Erdogan Shugaban kasar Turkiya domin halartar taron gyara dangantaka tsakanin kasashen Larabawa da musulmi tare da Amurka.
To amma abin tambaya a nan shi ne mine ne manufar Sarki Salman na gayyatar Shugabanin kasashen musulmi 17 zuwa birnin Riyad domin ganawa da Shugaban kasar Amurka?
Na farko, manufar Sarki Salam bn Abdul-aziz na wannan shiri, shi ne nuna irin karfin da masarautar Saudiya ke da shi a yankin, a yayin ziyara Shuganan kasar Amurka Donal Trump , Sarki Salman ya bukaci ya shirya wannan zama ne da zai hada Shugabanin kasashe 17 na Larabawa da musulimi tare da magabatan Amurka a birnin Riyad domin ya nunawa Shugaba Trump mahimancin kasar Saudiya wajen kare manufofin Amurka a gabas ta tsakiya, a hakikanin gaskiya shi ne nuna irin karfi da kuma matsayin Saudiya a Duniyar musulmi ga sabin Shugaban Amurka da ba shi da kwarewa a fagen Siyasa, duk da cewa babu tabas ko dukkanin kasashen da aka gayyata za su amince da wannan gayyata.
Na biyu kuma shine bude wani sabon babe a kan tsorantar da kasashen musulmi a kan jumhoriyar musulinci ta Iran su ji cewa kasar ta Iran Baraza ce a gare su,kuma su samu goyon bayan Amurka a kan wannan manufa, duk da cewa Gwamnatin Amurkan da ta gabata nada kyakkyawar alaka da kasar Saudiya kuma ta kakabawa Iran mafi tsananin takunkumi, to amma magabatan birnin Riyad na ganin cewa yarjejjeniyar nukiliyar zaman lafiyar da kasar Iran ta cimma da manyan kasashe biyar gami da kasar Jamus zai ragewa Iran din matsin lambar da take fuskanta daga kasashen Duniya,domin Saudiyar ta kasance daga kasashe da suka bayyana kiyayarsu karara game da wannan yarjejjeniya, a halin da ake cikin Sarki Salam ya sake da'awar cewa kasar Iran din na taimakawa ta'addanci a yankin inda ya bukaci Donal Trump da ya kakabawa Iran din mafi tsananin takunkumi, domin cimma wannan manufa magabatan birnin Riyad din na bukatar goyon bayan aminan kasashen saudiyan, domin haka ne ma magabatan na Riyad suka shirya wannan zama na kasashen musulmi da na Larabawa 17 domin ganawa da magabatan Amurka, da a tunanin su hakan zai sanya su cimma manufofinsu.
Manufa ta uku na shirya wannan taro a birnin Riyad shi ne kokari wajen raya kungiyoyin 'yan ta'adda tare da karfafa su, dangane da wannan batu, Zainab Sahlani 'yar majalisar dokokin kasar Iraki da ta fito daga jam'iyar Al-Ahrar ta bayyana cewa shirya irin wannan taro tare da halartar Shugaba Trump zai kara janyo rudani a tsakanin kasashen Larabawa da musulmi saboda manufar shirya wannan taro shi ne sake gina kungiyar 'yan ta'addar IS da kuma sauren kungiyoyin ta'addanci bayan kashin da suka sha a kasashen Iraki da Siriya.Amurka da Suadiya sun samar da kungiyoyin 'yan ta'adda ne a yankin gabas ta tsakiya domin kare manufofinsu, Sarki Salam zai shirya taron kasashen Laraba da musulmi 17 tare da Shugaban Trump na Amurka ne domin samar da wata sabuwar hadaka da za ta hana raunana kungiyoyin 'yan ta'adda musaman ma a kasashen Siriya da Iraki.