Atisayen Sojin Sama Tsakanin Kasashen Sudan Da Saudiyya
Rundunonin sojin saman kasashen Sudan da Saudiyya sun fara gudanar da wani atisayen soji na hadin gwiwa da nufin karfafa rundunar sojin saman kasashen biyu domin ci gaba da kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen.
Atisayen rundunar sojin saman kasashen biyu mai taken "Blue Shield 1" da zai kwashe tsawon makonni biyu, an fara gudanar da shi ne tun a ranar Laraba 29 ga watan Maris a yankin Meroe da ke arewacin birnin Khartoum fadar mulkin kasar Sudan. Alaka tsakanin kasashen Sudan da Saudiyya a cikin shekara guda ta kara karfi ne musamman ganin yadda kasar ta Sudan ta shiga cikin jerin kasashen da suke taimakawa mahukuntan Saudiyya a yakin da suka kaddamar kan kasar Yamen, duk da cewa manufar Sudan ta shiga cikin jerin kawayen Saudiyya da suke yakar kasar Yamen bata da bambanci da sauran kasashen kawancen, wato manufa ce kawai ta samun kudade daga mahukuntan Saudiyya.
A cikin 'yan watannin da suka gabata jami'an gwamnatocin Sudan da na Saudiyya musamman a bangaren siyasa da na tattalin arziki sun gudanar da ziyarar aiki a kasashen junansu, inda suka cimma matsaya kan matakai da dama, duk da cewa babbar manufar mahukuntan Sudan kan karfafa alaka da Saudiyya ita ce; samun damar bunkasa harkar tattalin arzikin kasarsu, yayin da manufar mahukuntan Saudiyya kan bunkasa wannan alakar ita ce samun damar yin tasiri a harkokin da suka shafi kasashen Afrika musamman Larabawa daga cikinsu.
A fili yake cewa ta hanyar amfani da kudi mahukuntan Saudiyya suke samun damar juya akalar mafi yawan kasashen da suke da alakar jakadanci da su, kuma a kan wannan tubalin siyasar ne kasar Sudan zata mika kai bori ya hau. Sakamakon haka ministan harkokin cikin gidan Sudan Usamah Faisal ya yi furuci da cewa: A halin yanzu kasar Saudiyya ta zuba hannun jari na tsaban kudi dalar Amurka biliyan 111 a Sudan, kuma ana ci gaba da kokarin ganin nan da shekaru hudu masu zuwa, kasar ta Saudiyya zata rubanya hannun jarinta a kasar ta Sudan.
Hakika ta irin wannan salon siyasa ne mahukuntan Saudiyya suke saurin yaudarar kasashe da dama na duniya, tare da saukin samun damar juya akalar shugabannin kasashen, kamar haka ne shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya yi furuci da cewa: Tsaron kasar Saudiyya shi ne kan gaba da tsaron kasar Sudan. Bugu da kari wannan atisayen soji da Saudiyya take gudanarwa a cikin kasar Sudan yana dauke da wani babban sako ga mahukuntan kasar Masar, saboda ana gudanar da atisayen ne a yankin dake kusa da kan iyaka da kasar ta Masar, kuma yau kimanin shekara guda ke nan da kai ruwa rana tsakanin mahukuntan Saudiyya da na Masar.
Wannan mataki da mahukuntan Saudiyya suka dauka na gudanar da atisayen soji na hadin gwiwa da kasar Sudan tare da zuba hannun jari a kasar, a fili yake cewa; Siyasa ce ta dan gajeren lokaci da zata yi saurin rushewa, kamar yadda hakan ya faru a kasashe da dama na yankin gabas ta tsakiya, kuma shugaba Umar Hasan Albashir yana sane da hakan, amma halin tsaka mai wuya da kasarsa ta shiga a fuskar tattalin arziki gami da matsin lambar da yake fuskanta a ciki da wajen kasar a bangarori da dama ya sanya alatilas ya rufe ido ya rungumi irin wannan salon siyasa maras karko.