Ganawar Sarkin Saudiyyah Da Theresa May A Riyad
(last modified Thu, 06 Apr 2017 12:27:45 GMT )
Apr 06, 2017 12:27 UTC
  • Ganawar Sarkin Saudiyyah Da Theresa May A Riyad

Firayi ministan kasar Birtaniya Theresa May ta gana da sarkin kasar Saudiyya a yammacin jiya a fadar Yamama da ke birnin Riyad.

Tashar talabijin ta kasar saudiyya ta bayar da rahoton cewa, a yayin ganawar ta su a yammacin jiya a fadar Yamama da ke birnin Riyadh, Theresa May da sarki Salman bin Abdulaziz sun tattauna kan kara bunkasa alaka a tsakaninsu, musamman a bangaren batutuwa na soji.

Theresa May ta tabbatar wa sarkin an Saudiyya da cewa za su ci gaba da agaza masa a yakin da yake yi da kasar Yemen tare da sayar masa da dukkanin makaman da yake bukata.

Daga lokacin da Saudiyya ta fara kaddamar da haria  kan al'ummar kasar Yemen shekaru 2 da suka gabata, ya zuwa yanzu Birtaniya ta sayar mata da makamai da suka haura na fan biliyan 3, wadanda akasarinsu ana amfani da su wajen kai hari a kan al'ummar kasar Yemen.