Pars Today
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyyya, ya bayyana cewa sun bai wa kasashen Saudiyya, Amurka, da Jamus da Faransa da kuma Ingila hoton bidiyon kisan dan jaridan Jamel Kashoggi.
An caccaki kasar Saudiyya dangane da tarihinta na take hakkokin bil'adama a Majalisar Kare Hakkokin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya a daidai lokacin da kasar take fuskantar tofin Allah daga dukkanin bangarori na duniya kan kisan gillan da ta yi wa dan jaridar kasar Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancinta dake Istanbul na kasar Turkiyya.
'Ya 'yan dan jaridan nan na Saudiyya da aka kashe, sun bukaci hukumomin Saudiyya dasu mika masu gawar mahaifinsu, ta yadda iyalansa zasu yi masa zaman makoki, kamar yadda suka sanar a gdian talabijin na CNN.
Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewar sama da kananan yaran kasar Yemen miliyan 7 ne suke fuskatar gagarumar barazanar yunwa a kasar sakamakon ci gaba da hare-haren wuce gona da irin da Saudiyya da kawayenta suke ci yi a kasar.
Tun bayan da shugaban kasar Gabon Ali Bango ya yi tafiya zuwa kasar Saudiyya a ranar Laraban makon da ya gabata, har inda yau take ba a kara jin duriyarsa ba.
Saudiyya ta yi watsi da bukatar Turkiyya na a mika mata wasu 'yan Saudiyyar su 18 da ake zargi da kashe dan jaridan nan Jamel Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyar na Santanbul.
Shugaban kasar Faransa Emanuel Macron ya nuna rashin amincewarsa da ra'ayin haramta sayarwa kasar saudia makamai. saboda kisan dan jarida Jamal Khashaggi.
Kwanaki kadan bayan da mahukuntan Saudiyya suka amsa cewa an kashe Jamal Khashoggi a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyyar na birnin Santanbul, sarki Salman da yarima mai jiran gado sun gana da iyalan dan jaridan da aka kashe.
Amurka ta sanar da wani matakinta na soke takardar iznin shiga kasar watau visa, ga 'yan Saudiyya da suke da hannu a kisan gillan da aka wa dan jaridan nan Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Santanbul yau da kusan mako uku.
Piraministan kasar Canada ya bayana shirin kasarsa na dakatar da yarjejjeniyar sayar da makamai ga kasar Saudiya