Saudiyya : Salmane Da Yarimansa Sun Gana Da Iyalan Kashoggi
(last modified Wed, 24 Oct 2018 05:55:17 GMT )
Oct 24, 2018 05:55 UTC
  • Sarki Salmane da  yariman mai jiran gado sun mika sakon ta\'aziyya ga iyalan Khshoggi
    Sarki Salmane da  yariman mai jiran gado sun mika sakon ta\'aziyya ga iyalan Khshoggi

Kwanaki kadan bayan da mahukuntan Saudiyya suka amsa cewa an kashe Jamal Khashoggi a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyyar na birnin Santanbul, sarki Salman da yarima mai jiran gado sun gana da iyalan dan jaridan da aka kashe.

Kamfanin dilancin labaren Saudiyya SPA ya rawaito labarin cewa Sarki Salmane da kuma yarima mai jiran gado Mohamed ben Salman sun gana da biyu daga cikin mambobin iyalan dan jaridan da aka kashe a fadar sarkin dake Riyad.

Iyalan mirigayin da aka gana dasu sun hada da dan Kashoggin din mai suna Salah, da kuma wani dan uwansa mai suna Sahel.

Sarki Salmane da  yariman mai jiran gado sun mika sakon ta'aziyya ga iyalan Khshoggi din a cewar labarin.

Saudiyya dai na ci gaba da fuskantar matsin lambar duniya akan ta bayyana hakikanin abunda ya faru har aka kashe dan jaridan a ranar 2 ga watan Oktoban nan a karamin ofishin jakadancinta na Santanbul a Turkiyya, saidai Saudiyyar ta nace kan cewa tsausayi ne auku, kuma ba tada wata masaniya akan inda gawar dan jaridan take.