Pars Today
Gwamnatin kasar Switzerland ta bakin ministan sharia na kasar ta bukaci a gurfanar da yan asalin kasar wadanda aka kama a cikin mayakan kungiyar Daesh a kasashen Siriya da Iraqi, a kasashen biyu.
Shugaba Bashar Al-Assad, na Siriya ya bayyana cewa har yanzu da sauren aiki game da yakin da kasarsa ke fama dashi.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, sun tattauana ta wayar tarho kan halinda kasar Siriya ke ciki.
Gwamnatin Amurka ta bada sanarwan cewa zata bukaci kawayenta su kawo daruruwan sojoji zuwa kasar Siriya bayan ta janya.
Kasashen Rasha, Turkiyya da kuma Iran, sun bayyana cewa shirin Amurka na janye dakarunta daga Siriya faduwa ce ta zo daidai da zama.
Gwamnatin kasar Siriya ta yi musayar fursinonin yaki da yan adawar kasar a dai-dai lokacinda za'a gudanar da taron tattaunawa a tsakaninsu.
Iran, ta ce kamfanoninta a shirye suke wajen sake gidan kasar Siriya da yaki ya daidaita.
Mayakan kungiyar yan ta'adda ta Daesh a gabacin kogin Furat na kasar Siriya sun fice daga yankin a yau Jumma'a.
MDD ta bada sanarwan cewa yara kanana da dama sun rasa rayukansu a sansanonin yan gudun hijira da ke arewa maso gabacin kasar Siriya sanadiyyar sanya.
Shugaba Bachar al-Assad, na Siriya ya jinjina wa yarjejeniyar kasuwancin da kasarsa ta cimma da Jamhuriya Musulinci ta Iran.