Gwamnatin Kasar Siriya Ta Yi Musayar Fursinoni Da Yan Adawa
Gwamnatin kasar Siriya ta yi musayar fursinonin yaki da yan adawar kasar a dai-dai lokacinda za'a gudanar da taron tattaunawa a tsakaninsu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Turkiya yana fadar haka, ya kuma kara da cewa an saki mutane da dama daga bangarorin biyu a jiya Talaya.
Wata kungiyar kare hakin bil'adama ta kasar Siriya da ke da cibiya a birnin Londan ta bayyana cewa an yi musayar fursinonin ne a garin Al-Bab da ke lardan Aleppo da ke arewa maso yammacin kasar Siriya. Kungiyar ta kara da cewa ko wani bangare ya saki fursinonin yaki 20 20 ne.
A gobe Alhamis ne 14 ga watan Febreru za'a gudanar da taron tattaunawa na gaba tsakanin gwamnatin kasar ta Sirioya da yan adawa a nbirnin Sochi na kasar Rasha, taro wanda kashe Rasha Iran da kuma Turkiya suke jagoranta don samar da zaman lafiya a kasar ta Siriya tun shekara ta 2017 da ta gabata.