Assad Ya Yaba Wa Yarjejeniyoyin Da Iran Da Siriya Suka Cimma
Shugaba Bachar al-Assad, na Siriya ya jinjina wa yarjejeniyar kasuwancin da kasarsa ta cimma da Jamhuriya Musulinci ta Iran.
A jiya Litini ne kasashen Siriyar da Iran suka sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyin 11 na huldar kasuwanci mai daurewa, wanda zai baiwa Iran damar zuba jari a kasar ta Siriya dake fama da yaki tun cikin shekara 2011.
Kamfanin dilancin labaren Siriya na Sana, ya rawaito shugaba Assad na cewa, yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma, ta zamo wani babban gimshiki na karya laggon wasu kasashen yamma na neman durkusar da tattalin arzikin kasashen.
Shugaba Assab wanda ke bayyana hakan a yayin wata ganawa da mataimakin shugaban kasar Iran, Eshaq Jahangiri, wanda ya kai ziyara a birnin Damascos jiya Litini, ya ce, yana da kyau bangarorin biyu su kara karfafa huldar dake tsakaninsu don hana kasashen dake son durkusar da Iran da Siriya su cimma manufarsu.
Daga cikin yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma har da gyaren wasu manyan gine gine da suka hada da tashar ruwa ta Tartous da Lattaquié, da kuma gina wata tashar samar da wutar lantarki mai karfin migawatt, 540.
Ko a watan Agusta da ya gabata ma kasashen Siriya da Iran sun cimma wata yarjejeniya soji a tsakaninsu.
Yarjejeniyoyin da bangarorin biyu suka cimma na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta kakaba wasu sabbin takunkumai kan Iran, a daidai lokacin da kuma wasu kamfanoni da manyan jami'an gwamnatin Siriya ke ci gaba da kasancewa karkashin takunkuman Amurka da kuma na wasu kasashen turai.
Iran dai ta kwashe shekaru da dama tana taimakawa kasar Siriya, musamman da man fetur da kuma hanyoyin samun kudade.
Kimanin dalar Amurka Biliyan 400 ne MDD, ta kiyasta cewa ana bukata wajen sake gina kasar Siriya da yaki ya daidaita.
Gwamnatin Siriya dake samun goyan bayan kasashen Rasha da Iran, a shekarun baya bayan nan ta yi nasara kwato wasu yankunanta daga hannun 'yan ta'adda na IS da kuma 'yan tada kayar baya inda a yau take rike da ikon kashi biyu cikin uku na fadin kasar.
Rikicin kasar Siriya dai ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 360,000 tare da tilasta wa rabin al'ummar kasar yin gudun hijira.