-
Mutane 5 Sun Mutu Sakamakon Harin Ta'addancin Al-Shabab A Kasar Somaliya
Jan 24, 2017 11:18Rahotanni daga kasar Somaliya sun bayyana cewar alal akalla mutane biyar sun rasa rayukansu kana wasu na daban kuma sun sami raunuka sakamakon harin ta'addancin da 'yan kungiyar Al-Shabab suka kai kudancin kasar ta Somaliya.
-
Kasar Burundi Ta Janye Batun Janye Sojojinta Daga Somaliya
Jan 21, 2017 11:53Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da gwamnatin kasar Burundi sun cimma yarjejeniyar biyan dakarun kasar Burundin da suke aiki karkashin tawagar Majalisar Dinkin Duniya wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar Somaliya, lamarin da ya sanya Burundin sanar da dakatar da shirinta na janye sojojin nata.
-
Kungiyar Alshabab Ta Kai Hari Kan Ofishin Majalisar Dinkin Duniya A Magadishou
Jan 04, 2017 17:48Kungiyar 'yan ta'addan Alshabab ta kaddamar da hari a kan babban ofishin majalisar dinkin duniya da ke birnin magadishou fadar mulkin kasar Somalia.
-
Sojojin Somaliya Da Dakarun Zaman Lafiya Na Afirka Sun Kwato Wani Yanki Daga Hannun al-Shabab.
Jan 04, 2017 12:33mayakan al-shabab sun ja da baya daga garin Mooragaabey da ke gundumar Bakool a kudancin kasar, saboda kutsawar da sojoji da dakarun Afirka su ka yi.
-
Harin Kunan Bakin Wake A Cibiyar Sojojin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Somalia Ya Kashe Mutane 3
Jan 03, 2017 07:31Wani dan kunan bakin wake ya tuka wata mota makare da boma bomai zuwa kusa da kofar shigar cibiyar sojojin tabbatar da zaman lafiya mafi girma a kasar Somalia, inda ya tarwatsa ta, ya kuma kashe akalla sojojin kasar somalia ukku.
-
An Kashe Wani Babban Jami'in Tsaro A Fadar Shugaban Kasar Somalia
Jan 01, 2017 14:47Wasu majiyoyin gwamnatin kasar Somalia ta bayyana cewa wani harbi da bindiga a fadar shugaban Somalia ya yi sanadiyya mutuwar mataimakin shugaban sojojin da suke kare fadar shugaban kasa.
-
Shugaban Burundi Yayi Barazanar Janye Sojojin Kasar Daga Somaliya
Dec 31, 2016 05:51Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza yayi barazanar janye sojojin kasar daga cikin tawagar dakarun kungiyar Tarayyar Afirka da suke kasar Somaliya matukar dai ba a biya su albashinsu ba.
-
Kenya: An Kara Wa'adin Hana Zirga-zirga a Kan Iyakar Kenya Da Somaliya
Dec 29, 2016 17:49Gwamnatin Kasar Kenya ta kara wa'adin hana kai da komowar a yankin Mandera da ke kan iyaka da kasar Somaliya.
-
Somalia: An Sake Dage Zaben Shugaban Kasar Somalia Zuwa Sabuwar Shekara
Dec 28, 2016 17:24An sake daga zaben shugaban kasa a kasar Somalia har zuwa watan Jeneru na shekara mai kamawa, wannan shine karo na hudu kenan da ake daga zaben saboda matsaloli na yan sayasar kasar.
-
Somaliya: A karo Na Hudu An Dage Lokacin Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa.
Dec 27, 2016 06:49An Dage Zaben Shugaban Shugaban Kasar Somaliya Daga Wannan Watan Na Decemba Zuwa Watan Janairu Na Shekara Mai Zuwa.