Kasar Burundi Ta Janye Batun Janye Sojojinta Daga Somaliya
Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da gwamnatin kasar Burundi sun cimma yarjejeniyar biyan dakarun kasar Burundin da suke aiki karkashin tawagar Majalisar Dinkin Duniya wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar Somaliya, lamarin da ya sanya Burundin sanar da dakatar da shirinta na janye sojojin nata.
Kafar watsa labaran Africanews ya bayyana cewar an sanya hannu kan yarjejeniyar ce tsakanin wakilan kungiyar AU din da wata tawaga ta jami'an kasar Burundi da suka hada ministocin harkokin waje da kuma na tsaro da tsaron lafiyar al'umma na kasar.
A kwanakin baya ne dai gwamnatin kasar Burundin ta yi barazanar janye sojojinta daga cikin tawagar sojojin kungiyar AU din da suke tabbatar da zaman lafiya a kasar Somaliya saboda rashin biyansu albashi da sauran hakkokinsu.
To sai dai sakamakon cimma wannan yarjejeniyar kungiyar AU din ta amince ta biya wadannan albashi da hakkokin.