Somalia: An Sake Dage Zaben Shugaban Kasar Somalia Zuwa Sabuwar Shekara
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15826-somalia_an_sake_dage_zaben_shugaban_kasar_somalia_zuwa_sabuwar_shekara
An sake daga zaben shugaban kasa a kasar Somalia har zuwa watan Jeneru na shekara mai kamawa, wannan shine karo na hudu kenan da ake daga zaben saboda matsaloli na yan sayasar kasar.
(last modified 2019-03-07T02:07:59+00:00 )
Dec 28, 2016 13:54 UTC
  • Somalia: An Sake Dage Zaben Shugaban Kasar Somalia Zuwa Sabuwar Shekara

An sake daga zaben shugaban kasa a kasar Somalia har zuwa watan Jeneru na shekara mai kamawa, wannan shine karo na hudu kenan da ake daga zaben saboda matsaloli na yan sayasar kasar.

Jaridar yanar gizo ta Allafrica ta bayyana cewa a tsarin zaben kasar Somalia wanda yanayin harkokin tsaron kasar ya tilasta masu, shi ne wakilai 14,025 wadanda shuwagabannin kabilu da larduna suka zaba sune suke zaben yan majalisar dokokin kasar, wadanda su kuma suke zaben shugaban kasa daga baya. 

A halin yanzu dai a cikin makonnin da suka gabata wadannan wakilai 14000 sun zabi  yan majalisun dokokin kasar guda biyu, amma zaben shugaban kasar ne har yanzun bai samu ba.

A yau Laraba 28 ga watan Decemba ne hukumar zaben kasar ta tsaida cewa  za'a gudanar da zaben na shugaban kasar,  amma a wannan karon ma hakan bai samu ba , don haka ne hukumar ta sake daga shi a karo na hudu zuwa 24 ga watan Jeneru na shekara ta 2017 mai kamwa.

Jakadan majalisar dinkin duniya na musamman a kasar ta Somalia Michael Keating ya bayyana cewa akwau fargaba da suke yi kan zaben na somalia, amma dai abu mafi muhimmanci shi ne an sami damar gudanar da mafi yawan zabubbukan, a halin yanzu na shugaban kasar ne ya gagara, amma ana fatan daga karshe za'a gudanar da zaben.