Kungiyar Alshabab Ta Kai Hari Kan Ofishin Majalisar Dinkin Duniya A Magadishou
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16099-kungiyar_alshabab_ta_kai_hari_kan_ofishin_majalisar_dinkin_duniya_a_magadishou
Kungiyar 'yan ta'addan Alshabab ta kaddamar da hari a kan babban ofishin majalisar dinkin duniya da ke birnin magadishou fadar mulkin kasar Somalia.
(last modified 2018-08-22T06:59:29+00:00 )
Jan 04, 2017 14:18 UTC
  • Kungiyar Alshabab Ta Kai Hari Kan Ofishin Majalisar Dinkin Duniya A Magadishou

Kungiyar 'yan ta'addan Alshabab ta kaddamar da hari a kan babban ofishin majalisar dinkin duniya da ke birnin magadishou fadar mulkin kasar Somalia.

Kamfanin dillancin labaran Reauters ya bayar da rahoton cewa, kakakin rundunar 'yan sanda ta kasar Somalia Nur Usman ya sanar a yau cewa, an tayar da wata mota da aka shakare da bama-bamai a kusa da babban ginin majalisar dinkin duniya da ke birnin Magadishou, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwa jami'an tsaro 4 da ke gadin wurin tare da jikkatar wasu.

Jim kadan bayan faruwar lamarin kungiyar Alshaba ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin kai harin a kan wadanda ta kira kafirai.

A ranar Litinin da ta gabata ma mayakan kungiyar sun kai hari kan sansanin dakarun wanzar da sulhu da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka, inda suka kashe uku daga cikin dakarun.