Pars Today
Gwamnatin kasar Jamus ta bada sanarwan dage takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar Turkia a shekara ta 2017 bayan da jami'an tsaron kasar Turkia suka kama wasu masu rajin kare hakkin bil'adama da yan jarida guda 6 suka tsare.
Kungiyar tarayyar Turai ta bayyana jin dadinta da matakin da mahukuntan Turkiyya suka dauka na dage dokar ta baci a kasar.
Kafofin yada labarai na gwamnatin Turkiyya, sun ce an dage dokar ta bakin da aka kafa a kasar tun cikin watan Yuli na shekara 2016, bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar.
Gwamnatin Turkiyya ta sanar da korar ma'aikata sama da 18,000 daga bakin aiki, wadanda mafi yawa daga cikinsu ma'aikatan tsaro ne.
Shugaba Hassan Rohani na Jamhuriya Musulinci ta Iran, ya taya, Recep Tayyip Erdoğan, murna kan sake zabensa a wani wa'adin mulki kasar Turkiyya.
Babban abokin hammayar Shugaba Recep Tayyip Erdogan a zaben Turkiyya, Muharrem Ince, ya amince da shan kayi a zaben shugaban kasar da aka kada a jiya Lahadi.
Rahotanni daga Turkiyya ne cewa, shugaba Recep Tayyip Erdogan, ne ke kan gaba a sakamakon zaben shugaban kasar da sama da kashi 58% na yawan kuri'a da aka kada a zaben na yau Lahadi.
Wata kotu a yammacin kasar turkiya ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai kan tsoffin sojojin kasar 104 bayan ta samesu da laifin kokarin juyin mulki wa halattaciyar gwamnatin kasar.
A yayin da duniya ke ci gaba da tir da kisan da sojojin yahudawan sahayoniya suka wa Palasdinwa 55 a zirin Gaza, kasashen Afrika ta Kudu da kuma Turkiyya sun janye jakadunsu a Israila.
Senatocin majalisar dattawan kasar Amurka uku sun gabatarwa majalisar bukatar a dakatar da mikawa kasar Turkiya jarage yaki samfurin F-35 da ta saya.