Jul 22, 2018 06:30 UTC
  • Jamus Ta Dage Takunkuman Tattalin Arzikin Da Ta Dorawa Kasar Turkia.

Gwamnatin kasar Jamus ta bada sanarwan dage takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar Turkia a shekara ta 2017 bayan da jami'an tsaron kasar Turkia suka kama wasu masu rajin kare hakkin bil'adama da yan jarida guda 6 suka tsare.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa bayan kama wani dan jarida mai takardun shaidar zama dan Jamus da wasu mafu fafutukan kare hakkin bil'adama, dangantaka tsakanin kasashen biyu yayi tsami.

A ranar Alhamis da ta gabata ce gwamnatin kasar Turkia ta dage doka ta bacin da ta kafa tun bayan wani kokarin juyin mulkin da aka yi na kifar da gwamnatun Rajab Tayyib Urdugan a cikin watan Yulin shekara ta 2016 bai sami nasara ba. Bayan haka ne gwamnatin kasar ta kafa doka ta baci wacce ta bawa gwamnatin damar kamawa da tsare dubban mutanen kasar wadanda take tuhuma da hannu cikin kokarin juyin mulkin. 

Gwamnatin Kasar Turkia ta zargi Fathullahi Ghulen wani dan kasar kuma malamin addini, mazaunin Amurka da hannu cikin kokarin juyin mulkin.

Tags