An Janye Dokar Ta Baci A Turkiyya
(last modified Thu, 19 Jul 2018 05:44:33 GMT )
Jul 19, 2018 05:44 UTC
  • An Janye Dokar Ta Baci A Turkiyya

Kafofin yada labarai na gwamnatin Turkiyya, sun ce an dage dokar ta bakin da aka kafa a kasar tun cikin watan Yuli na shekara 2016, bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar.

Kamfanin dilancin labaren Anadolu, ya rawaito cewa dokar ta bakin, wacce ita ce karo na 7 da aka tsawaita a ranar 19 ga watan Afrilu ta kawo karshe da misalin karfe 1:00 na dare agogon wurin a cikin daren jiya wayewar wannan safiyar ta Alhamis.

A ranar 20 ga watan Yuli na 2016 ne, hukumomin kasar suka kafa dokar ta baki ta tsawan watannin ukku, kuma tun lokacin ne ake ta tsawaita ta ba kakkautawa.

A makon da ya gabata ne gwammatin Turkiyyar, ta sanar da cewa ba za'a kara tsawaita dokar ta bakin ba.

A karkashin dokar ta bakin dai gwamnatin Turkiyya ta kame dubban ma'aikata da jami'an tsaro wadanda ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki wa Shugaba Recep Tayyib Erdogan, wanda bai yi nasara ba.