Erdogan Na Kan Gaba A Zaben Turkiyya
(last modified Sun, 24 Jun 2018 16:29:10 GMT )
Jun 24, 2018 16:29 UTC
  •  Erdogan Na Kan Gaba A Zaben Turkiyya

Rahotanni daga Turkiyya ne cewa, shugaba Recep Tayyip Erdogan, ne ke kan gaba a sakamakon zaben shugaban kasar da sama da kashi 58% na yawan kuri'a da aka kada a zaben na yau Lahadi.

Kamfanin dilancin labaren gwamnatin kasar na Anadolu, ya ce a yayin da Erdogan ke bukatar 50% don kada a je zageye na biyu, ya yi wa babban abokin hammayarsa fintinkau.

Dan takara na Social Demokrat, Muharrem Ince, ya samu kashi 21% na kuri'un da aka kada, a ci gaba da fitar da kwarya kwarya sakamakon zaben.

Saidai tun kafin fara fitar da sakamakon zaben, babbar jam'iyyar adawa ta kasar  ta yi korafin tafka magudi da kurai kurai a zabukan.

A safiyar yau Lahadi ne al'ummar kasar ta Turkiyya suka kada kuri'a a zaben shugaban kasa gami dana 'yan majalisar dokoki wanda shi ne irinsa na farko mafi tsarkakiya tun bayan hawan karagar mulkin Mista Erdogan a shekara 2003.