-
Ansarullah Ta Bayyana Kudurinta Na Ganin Zaman Lafiya Ya Tabbata A Kasar Yemen
Dec 08, 2018 18:20Daya daga cikin masu wakiltar kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen da aka fi sani da 'yan Huthy, ya bayyana cewa; Sun je kasar Sweeden ne domin ganin an samu zaman lafiya a Yemen
-
Ansarullah Sun Ki Amincewa Da Batun Mika Tashar Bakin Ruwa Ta Hudaydah
Dec 08, 2018 04:17Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta ki amincewa da bukatar da bangaren tsohon shugaban kasar Abd Rabbuh Mansur Hadi da ke samun goyon bayan Saudiyya suka gabatar mata na ta mika garin Hudaydah da kuma ikon sanya ido kan jiragen da suke sauka a filin jirgin sama garin Sana'a gare su a ci gaba da tattaunawar sulhun da ake yi.
-
Tattaunawa Neman Zaman Lafiya A Yemen
Dec 06, 2018 09:59A wani lokaci yau Alhamis ne ake fara wata tattaunawa a Sweden, domin lalubo hanyoyin kawo karshen rikicin kasar Yemen, wanda ya hadassa mutuwar mutane akalla 10,000 a cikin shekara hudu.
-
Yemen : 'Yan Houthis Sun Gindaya Sharadi Kafin Shiga Tattaunawa
Nov 30, 2018 04:18'Yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsis a Yemen, sun gindaya sharadin cewa, zasu shiga tattaunawar da za'ayi a Sweden, a shiga tsakanin MDD, muddin aka basu tabbaci akan tafiyarsu da dawowarsu tawagarsu cikin cikaken tsaro.
-
Amurka Na Kokarin Yin Kafar Ungulu Ga Shirin Tsagaita Wutan Kasar Yemen A Kwamitin Tsaro
Nov 28, 2018 17:29Amurka ta bukaci Kwamitin Tsaron MDD da ya dakatar da wani daftarin kudurin da aka gabatar da zai bukaci a gaggauta tsagaita wuta da cimma yarjejeniya a kasar Yemen, abin da ake ganinsa a matsayin kokarin Amurka na yin kafar ungulu ga kokarin da kasashen duniya suke yi wajen dakatar da wuce gona da irin Saudiyya a kan kasar Yemen din.
-
Kungiyar Red Crescent Ta Iran Ta Sanar Da Aniyarta Na Taimakawa Al'ummar Yemen
Nov 23, 2018 10:16Babban sakataren kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Iran, Muhammad Muhammadi Nasab ya bayyana aniyar kungiyar ta su ta kasantuwa a kasar Yemen don ba da agaji na gaggawa ga al'ummar kasar Yemen din da suke fuskantar matsaloli na rayuwa sakamakon ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da Saudiyya da kawayenta suke kai wa kasar.
-
Yemen : An Bukaci Masu Rikici Su Nisanci Asibitin Hodeida
Nov 23, 2018 03:50Mukadashin babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, kan harkokin jin kai, Mark Lowcock, da kuma babbar Daraktar asusun kula da yara na MDD, Unicef, Henrietta Fore, sun bukaci masu rikici a kasar Yemen dasu nisanci babban asibitin al-Thawrah na Hodeida.
-
Manzon MDD Na Tattaunawa Da Jami'an Gwamnatin Yemen A San'a
Nov 22, 2018 16:37Manzon musamman na majlaisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikicin Yemen na ci gaba da gudanar da tattaunawa tare da jami'an gwamnatin tseratar da kasa a San'a.
-
Yemen : Za'a Tattaunawa Tsakanin Masu Rikici A Watan Disamba
Nov 22, 2018 10:45Amurka ta sanar da cewa za'a yi tattaunawa a farkon watan Disamba mai zuwa, tsakanin bangarorin dake rikici da juna a kasar Yemen.
-
Masu Rikici A Yemen Sun Amince Shiga Shirin Samar Da Zaman Lafiya
Nov 19, 2018 16:44Bangarorin dake rikici a Yemen, sun sanar da amince wa da shirin tattaunawa na Majalisar Dinkin Duniya domin samar da zaman lafiya a kasar.