Tattaunawa Neman Zaman Lafiya A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34347-tattaunawa_neman_zaman_lafiya_a_yemen
A wani lokaci yau Alhamis ne ake fara wata tattaunawa a Sweden, domin lalubo hanyoyin kawo karshen rikicin kasar Yemen, wanda ya hadassa mutuwar mutane akalla 10,000 a cikin shekara hudu.
(last modified 2018-12-06T10:50:17+00:00 )
Dec 06, 2018 09:59 UTC
  • Tattaunawa Neman Zaman Lafiya A Yemen

A wani lokaci yau Alhamis ne ake fara wata tattaunawa a Sweden, domin lalubo hanyoyin kawo karshen rikicin kasar Yemen, wanda ya hadassa mutuwar mutane akalla 10,000 a cikin shekara hudu.

Tattaunawar a shiga tsakanin majalisar dinkin duniya, na samun halartar bangarorin dake rikici a kasar ta Yemen, da suka hada da 'yan Houtsis da kuma gwamnati mai murabus.

Rikici na tsakanin bangarorin biyu dai ya jefa wannan kasar ta Yemen a cikin bala'i mafi muni a duniya inda mutane kimanin miliyan 14 ke fusknatar barazanar yunwa a cewar MDD, 

Wanann dai ba shi ne karo na farko da bangarorin ke haduwa kan teburin tattaunawa ba, don ko a shekara 2016 sun yi wata tattaunawa ta tsawan kwanaki 108 a kasar Koweit , saidai aka watse ba tare da cimma wata matsaya ba.