Nov 23, 2018 03:50 UTC
  • Yemen : An Bukaci Masu Rikici Su Nisanci Asibitin Hodeida

Mukadashin babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, kan harkokin jin kai, Mark Lowcock, da kuma babbar Daraktar asusun kula da yara na MDD, Unicef, Henrietta Fore, sun bukaci masu rikici a kasar Yemen dasu nisanci babban asibitin al-Thawrah na Hodeida.

A wata sanarwar hadin gwiwa da bangarorin biyu suka fitar sun nuna damuwa akan halin tsaka mai wuya da abibitin ke fadawa a duk lokacin da masu rikicin ke yakar junansu.

Babban asibitin na Hodeida dai ya kunshi sashen kula da yara masu fama da matsalar karamcin abinci mai gina jiki ko tamowa da kuma sashen kula da marasa lafiya cikin gaggawa da kuma na kula da masu fama da cutar amai da gudawa ko Kwalera.

Bangarorin sun ce duk da cewa akwai wasu asibitocin a birnin na Hodaida dake aiki, amma ba za'a iya samun kamar yadda ake kula da sha'anin kiwan lafiya na jama'a ba a babban asibitin na al-Thawrah wanda ake daukan yaunin jama'a birnin na Hodeida da gewayensa ba.

Wannan kiran bangarorin dai na zuwa ne a daidai lokacin da wakilin MDD kan rikicin aksar ta Yemen, Martin Griffiths, ke ci gaba da tuntubar masu rikici a kasar domin kwatar da hankali kafin tattaunawar da ake sa ran yi a farkon watan Disamba mai zuwa.

 

Tags