-
AU Na Sa Ran Fara Aiki Da Yarjejeniyar Cinikaya A Watan Yuli
Feb 11, 2019 02:02Kungiyar tarayya Afrika, ta bayyana cewa tana sa ran kasashe mambobinta zasu fara aiki da yarjejeniyar cinikaya marar iyaka ta tsakaninsu a watan Yuli na shekaran nan ta 2019.
-
Cutar Ebola Ta Kashe Mutum 500 A Congo
Feb 11, 2019 01:40Bayanai daga Jamhuriya Demokuradiyyar Congo na cewa mutum 500 ne cutar Ebola ta yi ajalinsu a cikin watanni shida a gabashin kasar.
-
Nijar : Bazoum, Ne Dan Takaran Jam'iyya Mai Mulki A Zaben 2021
Feb 11, 2019 00:36Jam'iyyar PNDS-Tarrayya, mai mulki a Jamhuriya Nijar, ta tsaida Mal. Mohammed Bazoum, a matsayin dan takaranta a zaben shugaban kasar na 2021 idan Allah ya kai.
-
Al'Sisi Na Masar Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar AU
Feb 10, 2019 06:31Shugaban kasar Masar, Abdel fatah Al-Sisi, ya karbi shugabancin kungiyar tarayya Afrika na wannan karo a hukumance, daga hannun takwaransa na Ruwanda Paul Kagame.
-
Sudan Ta Kudu : Kiir, Ya Zargi Kasashen Yamma Da Kawo Cikas Ga Zaman Lafiyar Kasar
Feb 09, 2019 13:19Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, ya zargi masu bada taimako na kasashen yammacin duniya da gazawa wajen kin samar da kudaden da za'a yi amfani da su wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya wanda zai kawo karshen yakin basasar kasar da aka shafe sama da shekaru biyar anayi a kasar.
-
An Fara Taron AU, Karo Na 32 A Birnin Adis-Ababa
Feb 09, 2019 13:02Yau Asabar, shuwagabannin kasashen Afrika, sun fara taronsu na shekara-shekara, a birnin Adis Ababa, na kasar Habasha
-
Boko Haram Ta Kashe Sojoji 3 A Najeriya
Feb 09, 2019 12:11Rahotanni daga najeriya na nuni da cewa kungiyar Boko haram ta kashe sojojin kasar a wani hari data kai wani sansanin soji a arewa maso gabashin kasar.
-
Saliyo:Za A Aiwatar Da Daurin Rai Da Rai Ga Duk Wanda Aka Kama Da Laifin Fyade
Feb 09, 2019 01:43Shugaban Kasar Saliyo Julius Maada Bio ya bayyana saka dokar ta baci sakamakon cigaba da yawaitar matsalar fyade da cin zarafin kananan yara da ke faruwa a kasar, tare da hukuncin daurin rai da rai a kan duk wanda aka kama da aikata mumunar aika aikar.
-
An Sake Kai Harin Ta'addanci A Burkina Faso
Feb 08, 2019 00:37Rundinar Sojin kasar Burkina faso ta sanar da mutuwar mutum biyu a wani harin ta'ddanci da aka kai kan wata barikin jami'an tsaron jandarma dake yankin Kongussi a arewacin kasar.
-
Wade Ya Yi Kiran Kauracewa Zaben Senegal
Feb 07, 2019 23:42Tsohon shugaban kasar Senegal, Abdulaye Wade ya sake nanata kiran a kauracewa babban zaben kasar na ranar 24 ga watan nan na Fabrairu.