Cutar Ebola Ta Kashe Mutum 500 A Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35170-cutar_ebola_ta_kashe_mutum_500_a_congo
Bayanai daga Jamhuriya Demokuradiyyar Congo na cewa mutum 500 ne cutar Ebola ta yi ajalinsu a cikin watanni shida a gabashin kasar.
(last modified 2019-02-11T05:10:06+00:00 )
Feb 11, 2019 05:10 UTC
  • Cutar Ebola Ta Kashe Mutum 500 A Congo

Bayanai daga Jamhuriya Demokuradiyyar Congo na cewa mutum 500 ne cutar Ebola ta yi ajalinsu a cikin watanni shida a gabashin kasar.

Alkalumman da Kungiyar tallafawa yara ta Save the Children, ta fitar sun nuna cewa a cikin watanni shida da suka gabata akalla mutum 785 ne suka kamu da cutar, inda 502 kuma cutar ta yi ajalinsu.

A cewar kungiyar ta Save the Children kuma kashi guda cikin biyar na mutanen da cutar ta shafa yara ne 'yan kasa da shekara biyar.

A watan Janairu da ya gabata, yawan masu kamuwa da cutar ya haura daga 20 zuwa 40, kuma idan ba'a dauki kwararen matakan gaggawa ba annobar zata iya ci gaba har na tsawan wasu watanni shida, ko kuma duk cikin shakarar a cewar Darektar kungiyar Heather Kerr.

Mtsalar tsaro da rikice rikice a gabashin kasar, na daga ciikin ababen dake zama karfen kafa wajen murkushe cutar.