AU Na Sa Ran Fara Aiki Da Yarjejeniyar Cinikaya A Watan Yuli
Kungiyar tarayya Afrika, ta bayyana cewa tana sa ran kasashe mambobinta zasu fara aiki da yarjejeniyar cinikaya marar iyaka ta tsakaninsu a watan Yuli na shekaran nan ta 2019.
Da yake bayyana hakan, kwamishinan harkokin ciniki da masana'antu na kungiyar, Albert Muchanga, ya ce yana sa ran yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar, zai fara aiki a hukumance a watan Yulin bana.
Da yake jawabi ga manema labarai a gefen babban taron kungiyar karo na 32, da ya gudana a Addis Ababa na Habasha, Mista Muchanga ya ce ana sa ran kaddamar da yankin ne yayin taron kungiyar da za a yi a birnin Yamai na Jamhuriya Nijar.
Kwamishinan ya ce, yanzu, akwai kasashen nahiyar 12 da suka amince da yarjejeniyar, kuma kafin karshen taron kungiyar, suna sa ran wasu karin kasashe 2 za su amince.
Ya ce, ya zuwa ranar 21 ga watan Maris na bana, za a cika shekara guda da kaddamar da shirin, kuma suna sa ran za su cike adadin da aka kayyade na kasashe mambobi 21 da ake bukata kafin yarjejeniyar ciniki cikin 'yancin ta fara aiki.
Har ila yau, ya ce AU na sa ran kasashe mambobinta za su fara cire shingayen cinikayya a tsakaninsu tare da rage kudaden haraji.
Tarayyar Afrika dai na fatan yankin ciniki cikin 'yanci na Afrikar, zai bunkasa ci gaban bangarori masu zaman kansu a nahiyar, da kafa kungiyar masana'antu, domin sa ran fara aiki da shirin a wannan shekara.