-
Amurka Ta Kawo Karshen Neman Kama Madugun 'Yan Tawayen Kungiyar LRA A Afirka Ta Tsakiya
Mar 27, 2017 05:45Wani babban jami'in sojin kasar Amurka ya sanar da cewa sojojin kasar Amurkan sun dakatar da hare-haren da suke kai wa kungiyar ta'addancin nan ta Lord’s Resistance Army (LRA) a Tsakiyar Afirka duk da cewa har ya zuwa yanzu ba a kama madugun kungiyar ba Joseph Kony ba.
-
An Hallaka Wani Jigon Al-Qaida A Afganistan
Mar 26, 2017 05:44Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da hallaka wani babban jigon kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Qaida mai suna Qari Yasin a wani harin jirgi marar matuki a Afganistan.
-
Sabon Makircin Majalisar Dokokin Kasar Amurka Kan Kasar Iran
Mar 26, 2017 05:31Wasu gungun 'yan Majalisun Dokokin Amurka da suka fito daga manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu Democratic da Republican sun gabatar da daftarin kuduri da ke neman tsananta kakaba takunkumi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
-
Kamfanonin Inshora A Amurka Sun Bukaci Diyar Dala Biliyan 6 Daga Saudiyyah Kan Harin 11/9
Mar 25, 2017 06:46Wasu kamfanonin inshora a kasar Amurka, sun bukaci diyar dala biliyan daga Saudiyyah sakamakon asarar da suka yi biyo bayan kai harin 11 ga watan satumban 2001.
-
Amurka za ta girke sabin makaman yaki a Siriya
Mar 22, 2017 12:26Kasar Amurka za ta tura Sojoji dubu da kuma wasu sabin makaman yaki zuwa kasar Siriya
-
Amurka Da Biritaniya Sun Hana Shiga Jirgi Da Kwamfuta
Mar 22, 2017 05:23Amurka da Biritaniya sun haramtawa fasinjojin wasu kasashen Larabawa da Turkiyya shiga jirage masu zuwa kasashen da wasu kayayyakin lataroni.
-
Hukumar FBI Ta Musanta Zargin Trump Na Cewa Obama Yayi Wa Wayarsa Kutse
Mar 21, 2017 05:23Shugaban Hukumar Binciken Laifukan na Amurka (FBI), James Comey yayi watsi da zargin da shugaban kasar Donald Trump yayi na cewa tsohon shugaban Amurka Barack Obama yana masa kutse cikin wayarsa kamar yadda kuma ya ce suna gudanar da bincike kan yiyuwar tasirin da ake zargin Rasha ta yi cikin zaben shugaban kasar da ya gudana a watan Nuwamban bara.
-
An Samu Karuwar Kai Hare-Hare A Kan Masallatai A Kasar Amurka
Mar 19, 2017 06:39An samu karuwar kai hare-hare a kan masallatai da cibiyoyin musulmi a kasar Amurka a cikin wannan shekara ta 2017.
-
Yancin Mallakar Makami Musamman Bindiga Yana Ci Gaba Da Lashe Rayukan Jama'a A Amurka
Mar 18, 2017 14:40Cibiyar kididdiga kan hare-haren wuce gona da iri da makami karkashin dokar 'yancin mallakar makamai a kasar Amurka ta fitar da rahoton cewa: Hare-haren wuce gona da iri da makami sun lashe rayukan mutane akalla 20 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata a sassa daban daban na kasar.
-
An Sace Wata Na'urar Kwamfutar Jami'an Tsaron Amurka Dauke Da Wasu Bayanan Sirri
Mar 18, 2017 11:22Rahotanni daga kasar Amurka sun bayyana cewar an sace wata na'urar kwamfuta ta hannu mallakar jami'an tsaron farin kaya na kasar dauke da wasu bayanai na sirri masu matukar muhimmanci a birnin New York.