Amurka za ta girke sabin makaman yaki a Siriya
Mar 22, 2017 07:56 UTC
Kasar Amurka za ta tura Sojoji dubu da kuma wasu sabin makaman yaki zuwa kasar Siriya
A cewar daya daga Dakarun Kurdawa na Democratic Alliance na kasar Siriya, Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon na shirin aikewa da Sojoji dubu guda domin taimakawa Dakarun su kwace garin Rikka.
A yayin da yake zantawa da manema Labarai Sojin ya bukaci a sakaye sunansa ya kuma ce baya ga Sojoji dubu gida, Amurkan ta ce za ta tura makaman yaki,kama daga manyan tankokin yaki na zamani, Motocin Yaki masu silke, Rokoki,Bindigogi masu kemara da sauransu.
Wannan lamari na zuwa ne a yayin da sabon Shugaban Amurka Donal Trump ke sukar Gwamnatin Barak Obama kan yadda take kashe kudaden kasar a Siriya.
Tags