-
Amurka Ta Fice Daga Yerjejeniyar Shirin Nukliyar Kasar Iran
May 08, 2018 19:05Shugaban kasar Amurka Donald Trump Ya Bayyana Ficewar Kasar Amurka daga yerjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran wacee kasar ta Amurka da wasu manya manyan kasashen duniya 5 suka kulla tare da kasar ta Iran a shekara ta 2015.
-
A Yau Ne Trump Ya Ce Zai Sanar Da Matsayinsa Kan Yarjejeniyar Nukiliyan Iran
May 08, 2018 07:49Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, a yau Talata da misalin karfe 6 na yamma agogin GMT, zai sanar da matsayinsa dangane da yarjejeniyar nukiliyan Iran.
-
Rasha: Wajibi Ne A Kare Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
May 07, 2018 18:57Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergey Ryabkov ne ya bayyana haka a yau litinin sannan ya kara da cewa; Rasha tana son ganin dukkanin bangarorin yarjejeniyar sun ci gaba da aiki da ita
-
Qassemi: Amurka Za Ta Yi Nadamar Ficewa Daga Yarjejeniyar Nukiliya
May 07, 2018 11:11Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, ya bayyana cewar Amurka za ta yi nadama mai girma matukar ta fice daga yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran.
-
Sharhi: Manufofin Netanyahu Na Sake Tayar Da Maganar Shirin Nukiliyan Kasar Iran
May 05, 2018 05:19A ranar Litinin din makon da ya wuce ne, a ci gaba da aiwatar da bakar siyasar adawa da Iran da kuma kada kugen yakin yakarta, firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya gabatar da wasu hotuna da bayanai da ya ce wai suna nuni da shirin Iran na mallakar makaman nukiliya.
-
Sakataren MDD Ya Ja Kunne Dangane Da Watsi Da Yarjejeniyar Nukiliyan Iran
May 03, 2018 17:24Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ja kunne dangane da yin watsi da yarjejeniyar nukiliyan da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran, tun da dai babu wata yarjejeniyar da a halin yanzu ta fi ta, yana mai bayyana yarjejeniyar a matsayin wata nasarar diplomasiyya mai muhimmanci.
-
Zarif: Iran Na Da Hakkin Mayar Da Martani Idan Amurka Ta Fice Daga Yarjejeniyar Nukiliya
May 03, 2018 17:24Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da hakkin mayar da martani matukar dai Amurka, a matsayinta na wani bangare na yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma a shekara ta 2015, ta fice daga cikinta.
-
New York Times: Netanyahu Ya Jawo Baraka Tsakanin Amurka Da Kasashen Turai Kan Shirin Iran
May 02, 2018 17:44Jaridar New York Times da ake bugawa a kasar Amurka ta rubuta a shafinta na yanar gizo cewa, abin da Netanyu ya yi na nuna wasu hotuna da yake cewa sirri ne kan shirin Iran na nukiliya da kuma hankoronta na kera makman kare dangi, wannan lamari ya jawo baraka tsakanin Amurka da kasashen turai.
-
Iran Ta Mayar Da Martani Ga Kalaman Netanyahu Kan Shirin Nukiliyanta
May 01, 2018 05:28Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, yayi watsi da tuhumce-tuhumcen da firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu yayi kan Iran yana mai cewa babu wani abin da ke cikin kalaman Netanyahun in ban zuki ta malle da kuma kokarin maras fa'ida.
-
Putin da Mogherini Sun Yi Watsi Da Kalaman Netanyahu Kan Shirin Nukiliyan Iran
May 01, 2018 05:28Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da babbar jami'ar harkokin wajen Tarayyar Turai Federica Mogherini sun kara jaddada aniyarsu na goyon bayan yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran suna masu kiran firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu da ya girmama ta.