-
Rundunar Sojin Nijeriya: Sabon Faifan Boko Haram Farfaganda Ce Kawai
May 13, 2017 13:28Rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da barazanar da kungiyar Boko Haram ta yi cikin wani sabon faifan bidiyon da ta fitar inda ta yi barazanar kai hare-hare cikin birnin tarayyar Nijeriya, inda ta ce faifan bidiyon farfaganda ce kawai da kungiyar ta saba yi, don haka kada 'yan kasar su damu da su.
-
An Nada Sabon Kwamandan Sojin Rundunar Fada Da Boko Haram A Nijeriya
May 11, 2017 01:18Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da yin wasu sauye-sauyen wajajen aiki ga wasu manyan kwamandojinta ciki kuwa har da kwamandan Rundunar Zaman Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram, inda aka nada wa rundunar sabon kwamanda wanda zai maye gurbin Manjo Janar Lucky Irabor.
-
Gwamnatin Najeriya: An Saki "Yan Matan Chibok Ne Ta Hanyar Musayarsu Da 'Yan Boko Haram.
May 07, 2017 07:31A yau lahadi ne 'yan matan Chibok da aka saki ta hanyar musaya da 'yan boko haram daga kurkuku, za su gana da shugaba Muhammadu Buhari.
-
Boko Haram Ta Saki Wasu Karin 'Yan Matan Chibok 82 Da Ta Yi Garkuwa Da Su
May 07, 2017 01:05Majiyar fadar shugaban Nigeriya ta sanar da cewa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun saki wasu karin 'yan matan Chibok 82 da suka yi garkuwa da su tun a shekara ta 2014.
-
Rundunar Sojin Chadi Ta Tabbatar Da Kashe Sojojinta 9
May 06, 2017 12:48Rundinar sojin Chadi ta tabbatar a hukumance da kashe sojojinta tara da kuma jikkatar wasu 20 a yayin wani hari da 'yan ta'addan boko haram suka kai masu a garin Kaiga.
-
Mayakan Kungiyar Boko Haram Sun Kai Hari A Garin Kondoga Na Gabacin Jihar Borno
May 06, 2017 08:48Wasu majiyoyin tsaro a jihar Borno na tarayyar Nigeria sun bayyana cewa wasu yan kunan bakin wake biyu sun tarwatsa kansu a cikin mutane a jiya jumma a garin Konduga, wanda ya kai ga mutuwar mutane 5 fararen hula da kuma raunata wasu 6.
-
Sojoji Sun Hallaka 'Yan Kunar Bakin Wake 3 Dake Son Kai Hari Sansanin Soji A Maiduguri
May 04, 2017 06:53Sojojin Nijeriya sun hallaka wasu 'yan kunar bakin wake su uku da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne a daren jiya Laraba a lokacin da suka yi kokarin kai hari wani sansanin sojin a garin Maiduguri da ke jihar Borno.
-
Mayakan Kungiyar Boko Haram Sun Sace Yan Mata A Wani Gari A Kasar Kamaru
Apr 22, 2017 07:29Majiyar labarai daga kasar Kamaru ta bayyana cewa mayakan kungiyar Boko Haram ta sun kai hari a garin Bbreche daga arewacin kasar sun kuma sace yan mata 3 masu shekaru tsakanin 8-14.
-
Sojojin Nijeriya Sun Sami Nasarar Hallaka Wasu 'Yan Kungiyar Boko Haram 21
Apr 18, 2017 06:33Rundunar sojin Nijeriya ta ce sojojinta sun sami nasarar hallaka wasu mayakan kungiyar Boko Haram su 21 da kuma ceto wasu mutane 1,623 da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su bayan wani gumurzu a kauyen Jarawa na karamar hukumar Kale Balge da ke jihar Borno.
-
Unicef: Bokoharam Tana Amfani Da Kananan Yara Wajen Kai Hare-hare.
Apr 12, 2017 14:30Asusun kananan yara na majalisar dinkin duniyar, ya ce acikin wannan shekara ta 2017 amfani da yaran da kungiyar ta ke yi ya karu.