Rundunar Sojin Nijeriya: Sabon Faifan Boko Haram Farfaganda Ce Kawai
Rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da barazanar da kungiyar Boko Haram ta yi cikin wani sabon faifan bidiyon da ta fitar inda ta yi barazanar kai hare-hare cikin birnin tarayyar Nijeriya, inda ta ce faifan bidiyon farfaganda ce kawai da kungiyar ta saba yi, don haka kada 'yan kasar su damu da su.
Kakakin rundunar sojin Nijeriya Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau din na Asabar inda ya ce: "Mutumin da ke wannan kumfar baki cikin faifan bidiyon na daga cikin wadanda suka ci moriyar musayar da aka yi ta sakin 'yan matan Chibok 82, ba shi da wani katabus na iya yin komai, don haka ku yi watsi da wannan barazana tasa".
Har ila yau Janar Kukashekan ya bukaci 'yan kasar musamman 'yan jarida da su ci gaba da ba wa rundunar ta su hadin kai yana mai shan alwashin cewa sojojin za su ci gaba da murkushe ''yan Boko Haram din har sai sun ga bayansu, kamar yadda kuma za su ci gaba da kare rayukan 'yan kasar.
A jiya ne dai kungiyar Boko Haram din ta fitar da wani sabon faifan bidiyo inda a ciki aka nuna daya daga cikin kwamandojin kungiyar da aka sake da ya bayyana sunansa a matsayin Abu Dardah tare da wasu 'yan kungiyar su hudu inda yayi barazanar kai hare hare a birnin Abuja. A faidai bidiyo na biyu kuma an nuna wasu daga cikin ‘yan matan sakandaren Chibok 4 dauke da bindigogin AK 47, daya daga cikinsu tana fadin cewa sun ki yarda su koma wurin iyayensu ne saboda ba musulmi ba ne don haka suna kiransu da su musulunta kamar yadda kuma suka tabbatar da mubaya'arsu ga kungiyar ta Boko Haram.