Unicef: Bokoharam Tana Amfani Da Kananan Yara Wajen Kai Hare-hare.
(last modified Wed, 12 Apr 2017 19:00:20 GMT )
Apr 12, 2017 19:00 UTC
  • Unicef: Bokoharam Tana Amfani Da Kananan Yara Wajen Kai Hare-hare.

Asusun kananan yara na majalisar dinkin duniyar, ya ce acikin wannan shekara ta 2017 amfani da yaran da kungiyar ta ke yi ya karu.

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato Asusun kananan yaran na duniya na cewa; A cikin watanni uku ba farkon wannan shekarar kungiyar 'yan ta'addar ta bokoharam ta yi amfani da kananan yarar da su ka kai 27 a gabar tafkin Chadi a kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru da Cahdi.

Rahoton ya nuna cewa a tsawon shekarar 2016 da ta gabata, kungiyar ta yi amfani ne da kananan yara 30 wajen kai hare-hare.

Shugabar asusun na kananan yara a yankin yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya, ta bayyana cewa; yaran ba masu laifi ba ne, sun zama ragunan layyar kungiyar bokoharam ne, domin ana tilasta su ne aikata laifuka.