Rundunar Sojin Chadi Ta Tabbatar Da Kashe Sojojinta 9
Rundinar sojin Chadi ta tabbatar a hukumance da kashe sojojinta tara da kuma jikkatar wasu 20 a yayin wani hari da 'yan ta'addan boko haram suka kai masu a garin Kaiga.
Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasar, Kanal Azem Bermandoa ya sanar ta ce a bangaren makiya an hallaka 'yan boko haram 38 da kuma kauto makaman yaki masu yawa.
Harin na jiya Juma'a shi ne irinsa mafi da kungiyar boko haram ta kai a baya bayan nan, an kai shi ne barikin sojin Kaiga dake arewacin N'Djamina babban birnin kasar a kusa da iyaka da kasashen Kamaru, Najeriya da Nijar.
Yau kusan shekara biyu kenan da kasashen dake fuskantar barazanar kungiyar ke cewa sun karya laggon 'yan boko haram din, aman duk da hakan kungiyar na ci gaba da kai hare-haren sari ka noke ko na kunar bakin wake a nan da cen.
Tun dai da rikicin boko haram ya soma yau shakara takwas kimanin mutane 20,000 ne suka rasa rayukansu, kana wasu miliyan 2,6 suka kaucewa gidajensu don tsira da rayukansu.