-
Boko Haram Na Shirye Ta Tattauna Da Gwamnati Kan Sake Karin 'Yan Matan Chibok
Oct 17, 2016 02:16'Yan kwanaki bayan sako 'yan matan makarantar Chibok su 21 da kungiyar Boko Haram ta yi, gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa wani bangare na kungiyar sun sanar da aniyarsu ta ci gaba da tattaunawa da gwamnatin don sako karin wasu 'yan matan su 83 daga cikin sama da 200 da suka sace sama da shekaru biyu da suka gabata.
-
Boko Haram Sun Sako Wasu 'Yan Matan Chibok 21 Da Suke Rike Da Su
Oct 13, 2016 14:11Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa an saki wasu 'yan matan Chibok su 21 daga cikin sama da 217 da ke hannun 'yan kungiyar Boko Haram da suka sace su sama da shekaru biyu da suka gabata.
-
Sojojin Nijeriya Sun Hallaka Wasu Mata 'Yan Ta'adda Su 2 Kusa Da Sansaninsu A Gwoza
Oct 07, 2016 14:56Rundunar sojin Nijeriya sun sanar da kashe wasu 'yan mata masu kunar bakin wake a lokacin da suka yi kokarin kai hari kan wani sansanin sojin da ke gwarin Gwoza, na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriyan a jiya Alhamis.
-
Gwamnatin Nijeriya Ta Sanar Da Shirin Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Gidajensu
Oct 06, 2016 07:28Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ta gama shirin da ya kamata wajen fara mai da ‘yan gudun hijirar da suka gudu daga gidajensu sakamakon rikicin Boko Haram zuwa gidaje da garuruwansu.
-
Sojojin Nijeriya Sun Hallaka 'Yan Boko Haram 15 A Wani Gumurzu A Borno
Sep 23, 2016 14:11Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa dakarunta sun sami nasarar hallaka 'yan kungiyar Boko Haram su 15, sannan ta rasa wasu sojoji biyu a wani harin da 'yan Boko Haram din suka kai wa wani sansanin sojojin a jihar Borno.
-
Mafarauta Sun Sha Alwashin Kamo Shekau In An Ba Su Dama
Sep 20, 2016 04:52Kungiyar mafarauta ta Nijeriya ta sanar da cewa memebobinta a shirye suke su shiga dajin Sambisa da kuma kamo shugaban kungiyar 'yan ta'addan nan ta Boko Haram Abubakar Shekau da ransa matukar aka ba su izinin hakan.
-
Sojojin Nijeriya Sun Mayar Da Martani Ga Sabon Faifan Bidiyon Boko Haram
Sep 15, 2016 01:22Hedkwatar Tsaro ta Nijeriya ta bayyana barazanar da kungiyar Boko Haram ta yi ga shugaban kasar Muhammadu Buhari a matsayin wani wasan yara tana mai cewa sabon faifan bidiyon sallar Idi da kungiyar ta fitar a dajin Sambisa wani shure-shure ne wanda ba zai hana su mutuwa ba.
-
Jami'an Tsaron Nijeriya Sun Kama Wani Babban Mai Hada Bama-Bamai Wa Boko Haram
Sep 05, 2016 11:41Hukumar 'yan sandan ciki ta Nijeriya (DSS) ta sanar da kama wani kwararren mai hada wa kungiyar Boko Haram bama-bamai a kokarin da ya ke yi na shiga da zama sojan Nijeriya din.
-
Buhari Ya Ba Da Umurnin Kama Jami'an Da Ake Zargi Da Sace Abincin 'Yan Gudun Hijira
Sep 01, 2016 12:49Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ba wa 'yan sandan kasar umurnin kama jami'an gwamnatin da ake zargi da sace kayayyakin abincin da aka shirya kai wa ga 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya tarwatsa a arewa maso gabashin kasar don ya zamanto darasi ga masu tunanin yin haka nan gaba.
-
Gwamnati Da Sojojin Nijeriya Sun Mayar Da Martani Ga Sabon Bidiyon 'Yan Matan Chibok
Aug 14, 2016 12:51Gwamnati da rundunar sojin Nijeriya sun mayar da martani ga sabon faifan bidiyon da 'yan kungiyar Boko Haram suka fitar dangane da 'yan matan Chibok da suke ci gaba da rike su sama da shekaru biyu da sace su da aka yi daga makarantarsu.