Sojojin Nijeriya Sun Mayar Da Martani Ga Sabon Faifan Bidiyon Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11053-sojojin_nijeriya_sun_mayar_da_martani_ga_sabon_faifan_bidiyon_boko_haram
Hedkwatar Tsaro ta Nijeriya ta bayyana barazanar da kungiyar Boko Haram ta yi ga shugaban kasar Muhammadu Buhari a matsayin wani wasan yara tana mai cewa sabon faifan bidiyon sallar Idi da kungiyar ta fitar a dajin Sambisa wani shure-shure ne wanda ba zai hana su mutuwa ba.
(last modified 2018-08-22T06:58:55+00:00 )
Sep 15, 2016 01:22 UTC
  • Sojojin Nijeriya Sun Mayar Da Martani Ga Sabon Faifan Bidiyon Boko Haram

Hedkwatar Tsaro ta Nijeriya ta bayyana barazanar da kungiyar Boko Haram ta yi ga shugaban kasar Muhammadu Buhari a matsayin wani wasan yara tana mai cewa sabon faifan bidiyon sallar Idi da kungiyar ta fitar a dajin Sambisa wani shure-shure ne wanda ba zai hana su mutuwa ba.

A wani rahoto da ta buga jaridar Daily Trust ta Nijeriyan ta jiyo kakakin hedkwatar tsaro ta Nijeriyan, Birgediya Janar Rabe Abubakar yana cewa wannan barazana da ta yi ga shugaba Buhari wani wasan yara ne kawai wanda su kansu sun san ba za su iya ba.

Janar Rabe Abubakar ya ci gaba da cewa 'yan Boko haram din suna son su nuna wa  mutane cewa suna nan ne fa, duk kuwa da cewa su kansu sun san ba haka lamarin ya ke ba.

Kakakin hedkwatar tsaron ta Nijeriya ya kara da cewa fitar da wannan faifan bidiyo wata alama ce ta rauni da kungiyar take fama da shi yana mai cewa hanya guda kawai da suke da shi na bayyanar da kansu ita ce kafafen sadarwa na zamani wanda ke gidan kowa, yana mai cewa koda wasa faifan bidiyon ba taba damunsu ba don kuwa za su ci gaba da aikinsu har sai sun kawar da sauran gyauron 'yan kungiyar ta'addancin.

A jiya ne dai kungiyar Boko Haram din ta watsa wani faifan bidiyo da ke nuna sallar Idin da suka gudanar a masallatai inda a daya daga cikin masallatan wanda ya jagorancin sallar yayi barazanar kama shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da kuma cewa lalle kungiyar tana nan daram din ta.