Gwamnatin Nijeriya Ta Sanar Da Shirin Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Gidajensu
Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ta gama shirin da ya kamata wajen fara mai da ‘yan gudun hijirar da suka gudu daga gidajensu sakamakon rikicin Boko Haram zuwa gidaje da garuruwansu.
Shugabar hukumar kula da ‘yan gudun hijira da wadanda suka rasa matsugunansu ta Nijeriya (NCFRMI) Sadiya Faruq ce ta sanar da hakan a Abuja bayan taron da jami’an hukumar suka gudanar inda ta ce wannan shirin da aka ba shi sunan “Operation Back Home” wato shirin komawa gida sannan babban abin da za ta ba shi muhimmanci shi ne ganin alal akalla ‘yan gudun hijiran miliyan 2 sun koma gidajensu lafiya.
Mrs Faruq ta kara da cewa, baya ga mutanen da rikicin Boko Haram ya ritsa da su har ila yau kuma shirin zai shafi mutanen da suka rasa matsugunansu suka hada da wadanda rikicin makiyaya ya ritsa da su, da ma wadanda sauran bala’oi na dabi’a irin su ambaliyar da sauransu suka shafa.
Cikin ‘yan shekarun nan dai Nijeriya ta fuskanci matsaloli da dama da yayi sanadiyyar sanya miliyoyin ‘yan kasar zaman ‘yan gudun hijira a bangarori daban-daban na kasar.