Mafarauta Sun Sha Alwashin Kamo Shekau In An Ba Su Dama
Kungiyar mafarauta ta Nijeriya ta sanar da cewa memebobinta a shirye suke su shiga dajin Sambisa da kuma kamo shugaban kungiyar 'yan ta'addan nan ta Boko Haram Abubakar Shekau da ransa matukar aka ba su izinin hakan.
Kafar watsa labaran Premium Times ya jiyo shugaban bangaren tsaro na kungiyar mafarautar a Adamawa Garba Tarfa yana cewa wani adadi mai yawa na mafaratutar suna cikin shirin shiga dajin Sambisan don kamo Abubakar Shekau da kwamandojinsa, abin da kawai suke jira shi ne izini. Yana mai cewa sun san lunguna da kusurwar dajin sosai don haka kama Shekau din ba zai yi musu wahala ba.
Garfa Tarfa ya kara da cewa a watanni ukun da suka gabatan 'yan kungiyar ta su tare da hadin gwiwan sojojin Nijeriyan sun kai hare-hare dajin na Sambisa inda suka kwato sama da mata da kananan yara 500 daga hannun 'yan Boko Haram din; kamar yadda ya ce kuma a wadannan hare-haren kimanin 'yan Boko Haram 50 suka kashe ko raunana ko kuma kama su da mika su ga mahukuta.
A wata sabuwa kuma rundunar sojin Nijeriya ta bakin kakakinta Kanar Sani Usman Kukasheka ya tabbatar da cewa wasu mutane 6 sun mutu sakamakon wani harin kwantan bauna da 'yan Boko Haram din suka kai wa wasu ayarorin motoci da sojoji suke musu rakiya a yankin Sanda a hanyar Damboa zuwa Maiduguri. Yana mai cewa an kara daukar tsauraran matakan tsaro kamar yadda kuma ya ce kada mutane su dauki hakan a matsayin wata barazana.