-
Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Ta'addanci A Arewacin Iraki
Jul 26, 2017 06:24Wata Mota Shake da bama-bamai ta tarwatse a gabashin Takrit cibiyar jihar salahaddin dake arewacin kasar Iraki, lamarin da yayi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama.
-
Wani Bom Ya Tashi Da Rundunar Kungiyar AU A Kasar Somaliya
Jul 18, 2017 17:54Rahotanni daga kasar Somaliya sun jiyo wasu majiyoyin tsaron kasar suna fadin cewa wani bam da aka dana ya tarwatsa wata motar soji da take dauke da dakarun kungiyar Tarayyar Afirka (AMISOM) a kudancin kasar.
-
Mutane 3 Ne Suka Rasu Bayan Tashin Wani Bam A Kusa Da Birnin Magadishu Na Somalia
Jul 13, 2017 06:53Tashar television ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto wata majiya daga birnin Magadishu babban birnin kasar Somalia tana cewa an tada bom a cikin wata mota a kusa da birnin wanda ya yayi sanadiyyar mutuwar mutane 3 da kuma raunata wasu 8.
-
Tashin Bam Ya Hallaka Mutane A Birnin Bangazin Libiya.
Jul 07, 2017 11:17Wani Bam ya Tashi a gefen Hanyar ficewar Dakarun tsaron Libiya a garin Bangazi dake gabashin kasar, lamarin da yayi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama
-
Tashin Bom Ya Kashe Mutane A Kasar Kenya Kusa Da Kan Iyaka Da Somaliya
Jun 27, 2017 19:03Wani bom da aka bisine a gefen hanya a yankin gabashin kasar Kenya kusa da kan iyaka da Somaliya ya kashe mutane 8 kuma hudu daga cikinsu kananan yara 'yan makaranta.
-
Somaliya: Mota Mai Makare Da Bama-bamai ta Fashe A Birnin Magadishu
Jun 22, 2017 18:54Rahotanni sun ce a kalla mutane hudu ne su ka mutu a sanadiyyar harin
-
Irakawa Akalla 11 Ne Suka Yi Shahada A Wani Ta'addanci Da Aka Kai Kasar Iraki
May 30, 2017 06:55Harin ta'addanci ta hanyar tarwatsa wata mota da aka makare da bama-bamai a yankin Karadah da ke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki yayi sanadiyar shahadar mutane akalla 11 tare da jikkatan wasu fiye da 50 na daban.
-
'Yan Sandan Kenya 5 Sun Mutu Sakamakon Harin 'Yan Ta'addan Al-Shabab
May 25, 2017 18:09Rahotanni daga kasar Kenya sun bayyana cewar wasu 'yan sandan kasar su biyar sun rasa rayukansu sakamakon wasu hare-hare da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta al-Shaba na kasar Somaliya suka kai musu kusa da kan iyakan kasar Kenyan da Somaliya.
-
Akalla Mutane 19 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Wasu Abubuwa A Birnin Manchester
May 23, 2017 05:50Rahotanni daga birnin Manchester na kasar Ingila sun bayyanar cewar alal akalla mutane 19 sun rasa rayukansu kana wasu kuma kimanin 50 sun sami raunuka sakamakon fashewar wasu abubuwa a cibiyar raye-raye ta Manchester Arena da ake ganin wani hari ne na ta'addanci.
-
Fashewar Wani Abu A Yankin Darfur Ta Kudu Da Ke Kasar Sudan Ya Janyo Hasarar Rayuka
May 22, 2017 06:17Wani abu ya fashe a wani wajen ajiyar kayayyaki a garin Nyala fadar mulkin lardin Darfur ta Kudu da ke kasar Sudan lamarin da ya janyo hasarar rayukan mutane akalla 5 tare da jikkata wasu fiye da 60 na daban.