Somaliya: Mota Mai Makare Da Bama-bamai ta Fashe A Birnin Magadishu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21580-somaliya_mota_mai_makare_da_bama_bamai_ta_fashe_a_birnin_magadishu
Rahotanni sun ce a kalla mutane hudu ne su ka mutu a sanadiyyar harin
(last modified 2018-08-22T11:30:17+00:00 )
Jun 22, 2017 18:54 UTC
  • Somaliya: Mota Mai Makare Da Bama-bamai ta Fashe A Birnin Magadishu

Rahotanni sun ce a kalla mutane hudu ne su ka mutu a sanadiyyar harin

Kamfanin dIllancin Labarun Reuters ya ambato 'yan sanda a birnin na Magadishu,suna cewa motar ta tarwatse ne a bakin kofar ofishin 'yan sanda na gundumar " Wa Biry", wanda baya ga asarar rayuka, wasu motoci masu yawa sun kone.

Yankin na Wa biry, yana daya daga cikin yankunan da su ka fi cikowa a cikin babban birnin kasar ta Somaliya.

A jiya laraba ma dai wata motar mai makare da bama-bamai ta tarwatse a wani hotel da ke tsakiyar Magadishu wanda ya ci rayukan mutane 9.

Kungiyar 'yan ta'adda ta al-shabab ta dauki alhakin kai hare-haren biyu.