Wani Bom Ya Tashi Da Rundunar Kungiyar AU A Kasar Somaliya
Rahotanni daga kasar Somaliya sun jiyo wasu majiyoyin tsaron kasar suna fadin cewa wani bam da aka dana ya tarwatsa wata motar soji da take dauke da dakarun kungiyar Tarayyar Afirka (AMISOM) a kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xianhua na kasar China ya ba da rahoton cewa lamarin ya faru ne a yankin Shabelle da ke kudancin kasar Somaliyan a yau din nan Talata din aka ce wani adadi na sojojin Somaliya da suke cikin motar sun sami raunuka.
Kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab dai ta dauki alhakin kai wannan harin, sai dai kuma jami'an tsaron kasar sun ce tuni suka gano wasu mutane biyu da ake zargin 'yan kungiyar ce wadanda kuma suke da hannu cikin wannan harin na ta'addanci, inda suke ci gaba da nemansu don kama su.
A bangaren guda jami'an tsaron kasar Somaliyan sun sanar da kama wata mota makare da bama-bamai da makamai a wani yanki da ke kan iyakar kasar da kasar Kenya. Ana zargin 'yan ta'addan suna shirin shiga da motar kasar Kenya ne don gudanar da ayyukan ta'addanci a can.