Tashin Bam Ya Hallaka Mutane A Birnin Bangazin Libiya.
Wani Bam ya Tashi a gefen Hanyar ficewar Dakarun tsaron Libiya a garin Bangazi dake gabashin kasar, lamarin da yayi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama
Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto majiyar tsaron Libiya a wannan safiya ta juma'a na cewa akalla Mutane 5 suka rasa rayukansu yayin da wasu 18 na daban suka jikkata sanadiyar tashin Bam a gefen babbar hanyar Asibitin Jamhoriya dake anguwar Sabiri na garin Bangazi dake gabashin kasar.
Majiya ta ce kungiyoyin 'yan ta'adda ne suka dasa wannan Bam a gefen hanyar ficewar Jami'an tsaron, a daren larabar da ta gabata ce Dakarun tsaron Libiya suka sanar da tsarkake birnin Bangazi daga mamayan 'yan ta'adda bayan kwashe shekaru uku ana fafatawa.
Libiya dai ta fada cikin rikici ne tun bayan kifar da Gwamnatin Kanal Mu'amar Kaddafi a shekarar 2011.