Jun 04, 2018 18:21
Kasar Italiya ta sanar da cewa ba za ta ci gaba da zama abin da ta kira sansanin 'yan gudun hijirar da suke shigowa Turai ba, tana mai shan alwashin daukar tsauraran matakan wajen rage 'yan gudun hijirar da suke shigowa kasar da kuma mayar da wadanda suka riga da suka shigo kasar.