Majalisar Kasar Libya Na Son Ganin An Kori Jakadan Kasar Italiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32703-majalisar_kasar_libya_na_son_ganin_an_kori_jakadan_kasar_italiya
Majalsiar dokokin kasar ta Libya ta zargi Jakadan Italiya da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar don haka ta bukaci ganin an kore shi.
(last modified 2018-08-22T11:32:13+00:00 )
Aug 10, 2018 06:28 UTC
  • Majalisar Kasar Libya Na Son Ganin An Kori Jakadan Kasar Italiya

Majalsiar dokokin kasar ta Libya ta zargi Jakadan Italiya da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar don haka ta bukaci ganin an kore shi.

 Kwamitin da yake kula da harkokin waje na Majalisar dokokin Libya, ya yi tir da yadda jakada giuseppe perronei ya bukaci da a dage lokacin yin zabe a kasar, tare da bayyana hakan a matsayin abin da ya sabawa aikin diplomasiyya.

Kwamitin na Majalisar dokokin kasar ta Libya ya bayyana Jakadan Italiya a matsayin wanda ba a maraba da shi a cikin kasar.

Jakadan na Italiya ya fada wa tashar talabijin din kasar ta Libya Ruhul Watan cewa baya goyon bayan a yi zabe a kasar a wannan lokacin.