Libiya Ta Zarki Wasu Kasashe Da Kokarin Jibke Sojoji A Cikin Kasar
Kakakin Sojojin Libiya ya zarki wasu kasashen turai da kokarin tura sojojinsu cikin kasar da nufin yaki da kwararen bakin haure.
Ahmad Mismari mai magana da yawun Rundunar tsaron kasar Libiya ya ce wasu kasashen Turai musaman ma kasar Italiya na kokarin turo sojojinta cikin kasar bisa da'awar yaki da kwararar baki haure zuwa kasashen Turai, kasar Italiya dai ta ce tana son tura sojojinta yankin Gat dake kudu maso yammacin kasar Libiya da nufin hana kwararan bakin hure zuwa kasar.
Ahmad Mismari ya bayyana wannan bukata ta Italiya a matsayin karya dokokin kasa da kasa da kuma keta hurumin kasar Libiya, sannan ya ce Sojojin Libiya na nazari kan yadda za su kalublanci sojojin kasar Italiya, saboda hukumomin kasar Italiyan sun dauki wannan mataki ne ba tare da tuntubar hukumomin kasar Libiya.
Tun bayan kawo karshen gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a Libiya a shekara ta 2011 kungiyoyin 'yan tawayen kasar suka dauki matakin mamaye yankunan da suke dauke da rijiyoyin man fetur na kasar ta Libiya, inda suka azurta kansu cikin dan gajeren lokaci, kafin rundunar sojin kasar ta fatattake su tare da kwace iko da yankunan.