Kasar Faransa Ta Kira Jakadanta A Roma Ya Dawo Gida
(last modified Thu, 07 Feb 2019 18:18:33 GMT )
Feb 07, 2019 18:18 UTC
  • Kasar Faransa Ta Kira Jakadanta A Roma Ya Dawo Gida

Gwamnatin kasar Faransa ta bukaci jakadan kasar da ke birnin Roma na kasar Italiya ya dawo gida saboda a binda ta kira shishigi wanda Italiya take yi a cikin harkokin cikin gidan kasar.

Kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa ya nakalto majiyar ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa tana fadar haka a yau Alhamis a wani bayanin da ta fitar dangane da hakan. 

Majiyar ta kara da cewa gwamnatin kasar Faransa ta dau wanann matakin ne don goyon bayan da gwamnatin kasar Italiya ta bawa masu zanga-zangar kin jinin jarin hajja a kasar wadanda aka fi sani da masu farmaran ruwan goro. 

Rikici tsakanin kasar Faransa da kuma Italiya ya kara tsanani ne bayan da Luigi di Maio mataimakin Firai ministan kasar Italiya ya gana da wakilan masu kin jinin tsarin jarin hujja ta kasar Faransa a wani wuri a birnin Paris a wani lokaci a kwanakin da suka gabata. 

Masana sun ce wannan shine sabani mafi tsanani tsakanin Faransa da Italiya tun bayan yakin duniya na biyu. A ranar Talatan da ta gabata ce mataimakin Firai ministan ya bayyana hotunan ganawarsa da shuwagabannin masu yaki da tsarin jari haujja a kasar ta Faransa.