Italiya Ta Dauki Mataki Kan Bakin Haure
Gwamnatin Italiya ta nemi taimakon kungiyar Nato game da hana shigar bakin haure cikin kasar
Hukumar gidan radio da talabijin na kasar Iran ta nakalto Matto Salvini ministan cikin gidan kasar Italiya na cewa gwamnati ta nemi kungiyar tsaron Nato ta taimaka mata wajen kalubalantar bakin haure dake shiga cikin kasar ta iyakokin kudancin kasar daga tekun Meditaraniya, sannan kuma ta gargadi kungiyoyin kare hakkin bil-adama da su guji taimakawa bakin hauren da kuma bin diddigin al'amuransu a gabar tekun ruwan na Italiya.
Ministan cikin gidan na Italiya ya tabbatarwa kungiyoyin fararen hula da na kare hakin bil-adama dake kwashe bakin hauren daga Tekun Meditaraniya suna isar zuwa gabar tekun ruwa na italiya cewa a halin yanzu tashar ruwansu a rufe take.
A ranar Lahadin da ta gabata ma, kasar Italiya ta ki karbar wasu jiragen ruwa na kungiyoyin fararen hula dake taimakawa bakin haure dauke da mutun 629, bayan kwashe kawanaki uku jiragen ruwan na yawo kan ruwa, daga karshe wasu jragen ruwan yaki biyu na kasar Italiya sun raka su zuwa kasar Spainiya.
A makun da ya gabata ce Piraministan kasar Italiya ya tabbatarwa Majalisar dokokin kasar cewa zai dauki kwararen matakai na hana shigar bakin haure cikin kasar.