Pars Today
Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai gudanar da zaman gaggawa don tattauna batun rikicin da ke faruwa a kasar Palasdinu a gobe Litinin.
Rahoto na uku wanda babban sakataren majalisar dinkin duniya ya gabatarwa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan shirin Nukliyar kasar Iran a cikin yerjejeniyar tsakanin kasashe 5+1, wanda kuma yake kunshe cikin kudirin kwamitin tsaron na 1231 ya nuna cewa Iran tana rike da alkawarinta .
Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya, ya bukaci kasashen Djibuti da Eritrea da su magance rikicin Iyakokinsu ta hanyar shawarwari.
Mayakan Ansarullah na kasar Yemen, sun maida martani akan sansanonin sojojin Saudiyya da ke Gundumomin Asir da Najran.
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau din nan Alhamis, yayi Allah wadai da kuma kakkausar suka ga harin ta'addancin da aka kai Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Komitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya a safiyar yau ya yi shiru na minti guda don tunawa da Iraniyawan da suka rasa rayukansu a hare haren ta'addancin guda biyu da aka kai a nan birnin Tehran
Koriya ta Arewa ta yi watsi gaba daya da sabbin takunkumin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sanya wa wasu kamfanoni da jami'an kasar, tana me shan alwashin ci gaba da shirin nukiliya da makamanta masu linzami ba tare da bata lokaci ba.
Kwamitin tsaro na MDD ya yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da gwajin makamin mai linzamin da Koriya ta Arewa ta yi a baya bayan nan, tare da shan alwashin daukan kwararan matakai kan gwamnatin ta Pyongyang.
Kwamitin tsaron MDD ya fara gudanar da taro kan yanayin da Al'ummar kasar Siriya ke ciki a birnin New York na kasar Amurka.
Kwamitin Tsaron MDD Yayi Barazanar Sanya Sabin Takunkumi ga Koreya Ta Arewa