Kwamitin Tsaron MDD Ya Fara Taro Kan Kasar Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19866-kwamitin_tsaron_mdd_ya_fara_taro_kan_kasar_siriya
Kwamitin tsaron MDD ya fara gudanar da taro kan yanayin da Al'ummar kasar Siriya ke ciki a birnin New York na kasar Amurka.
(last modified 2018-08-22T11:30:01+00:00 )
Apr 27, 2017 18:07 UTC
  •  Kwamitin Tsaron MDD Ya Fara Taro Kan Kasar Siriya

Kwamitin tsaron MDD ya fara gudanar da taro kan yanayin da Al'ummar kasar Siriya ke ciki a birnin New York na kasar Amurka.

A marecen yau Alkhamis ne Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara gudanar da taro kan halin da Al'ummar kasar Siriya ke ciki a birnin New York na kasar Amurka.

Bayan irin kashin da kungiyoyin 'yan ta'adda ke sha a hanun Dakarun kasar Siriya,Amurka ta zargi Gwamnatin Siriya da kai harin makami mai guba kan fararen hula a yankin Khan Shaihun dake kalkashin ikon 'yan ta'adda, lamarin da ya sanya Amurkan ta kai harin makami mai lizzami  a sansanin Jiragen saman yaki na kasar Siriya a ranar 7 ga watan Avrilun da ya gabata, saidai hakan ya sanya dakarun kasar Siriyan kara kaimi wajen fadada hare-haren su kan 'yan ta'addar ISIS a yankin Humus.

Harin makamai mai Lizzami na kasar Amurka na zuwa ne a yayin da magabatan Siriya ke kira da a gudanar da bincike kan wadanda suka yi amfani da makami masu guban kan fararen  a yankuna daban daban dake kalkashin ikon 'yan ta'adda a kasar ta Siriya.