Matsayin Kwamitin Tsaron MDD Kan Kasar Koreya Ta Arewa
Kwamitin Tsaron MDD Yayi Barazanar Sanya Sabin Takunkumi ga Koreya Ta Arewa
Tashar Telbijin din Press Tv dake watsa Shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa a jiya Alkhamis Kwamitin tsaron MDD ya ce zai sanya sabin takunkumi a kan kasar Korewa ta Arewa.
Cikin sanarwar da ya fitar, Kwamitin tsaron MDD ya ce kwajin makamai masu lizzami da Kasar Korewa ta arewa ta yi ya sabawa dokar kasa da kasa, kuma ci gaba da aiyukan Makamashin nukiliyar na kasar ya zanyo tayar da jijiyoyin wuya a yankin.
Shugaba Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa ya ce matukar Amurka ta kuskure ta kai wa kasar sa hari za su mayar da martani.
Magabatan Korewa ta Arewan sun bayyana ce shirin Makamashin nukiliya da kuma makami mai Lizzami na Gwamnatin Pyongyang na kare kasar ne daga baranzar Amurka.