Kwamitin Tsaro Zai Dauki Matakai Kan Koriya Ta Arewa
Kwamitin tsaro na MDD ya yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da gwajin makamin mai linzamin da Koriya ta Arewa ta yi a baya bayan nan, tare da shan alwashin daukan kwararan matakai kan gwamnatin ta Pyongyang.
A sanarwar bai daya da kasashe mambobin kwamitin cikin har da China suka fitar a jiya Litinin, kwamitin ya ce zai dauki matakai kan koriya ta Arewa ciki har da kakabawa shirin nukiliyarta takunkumi.
Koriya ta Arewa dai ta yi gwajin makaman nukiliya biyu da kuma gomman masu linzami daga farkon shekara 2016 data gabata zuwa yanzu.
Kuma duk hakan jerin takunkuman da aka kakaba ma ta karkashin jagorancin Amurka da MDD, ya gaza yin tasiri wajen dakatar da kokarinta na kera makaman.
A ranar lahadi data gabata ce gwamnatin Pyongyang ta harba wani makamin nukiliya wanda ya tayar da hankalin duniya.