-
Libya: Halifa Haftar Ya YI Gargadi Akan Tura Sojojin Waje Zuwa Yankin Kudancin Kasar
Jun 30, 2018 11:04Kamfanin dillancin labarun (AFP) ya ambato kwamandan sojojin Libya Janar Halifa Haftar yana cewa; Fakewa da batun fada da 'yan ci-rani ba zai zama dalilin aikewa da sojojin kasashen waje zuwa kudancin kasar ba
-
Libya: Haftar Ya Bada Sanarwar Kwace Garin Durnah Daga Hannun Yan Ta'adda
Jun 29, 2018 06:44Janar Halifa Haftar mai ritaya, wanda kuma yake iko da gabacin kasar Libya ya bada sanarwan cewa dakarunsa sun kwace garin darne daga hannun yan ta'adda a yankin.
-
Libiya Ta Yi Watsi Da Shawara Turai Kan Tantance Bakin Haure
Jun 28, 2018 05:22Kwamitin kare hakkin bil adama a Libiya, ya yi watsi da yunkurin kasashen Turai na kafa sansanonin tantance bakin haure a kasar.
-
Zaman Lafiya A Kasashen Yankin Sahel Zai Rage Kwararan 'Yan Gudun Hijira Zuwa Turai
Jun 27, 2018 12:29Shugaban hukumar kolin kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Wanzar da zaman lafiya da sulhu musamman a kasashen yankin Sahel zai taimaka wajen ragen kwararar 'yan gudun hijira zuwa kasashen Yammacin Turai.
-
Kamfanin Man Fetur Na Kasar Libya Bai Amince Da Mika Rijiyoyin Man Na Gabacin Kasar Ga Majalisar Tabruk Ba
Jun 26, 2018 19:01Kamfanin man fetur na kasar Libya ya yi Allawadai da mikawa majalisar dokokin gwamnatin gabacin kasar da ke Tabruk rijiyoyin mai na gabacin kasar.
-
An Bukaci Tallafin Kudade Don Tabbatar Da Zaman Lafiya A Niger, Mali Da Libya
Jun 26, 2018 19:00Shugaban hukumar yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ya bukaci tallafin kudade don ganin an dawo da zaman lafiya a kasashen Mali, Niger da kuma Libya.
-
Libiya Ta Yi Barazanar Rufe Iyakarta Da Tunisia
Jun 24, 2018 15:21Mahukuntan Libiya sun yi barazanar rufe iyakar kasar da Tunisia, muddun dai ci gaba da cin zarafin matafiyan kasar a Tunisia ya ci gaba.
-
An Cabke 'Yan Ta'addar ISIS Uku A Gabashin Libiya
Jun 23, 2018 19:01Kakakin ma'aikatar tsaron garin Shahhat na gabashin Libiya ya sanar da cabke 'yan ta'addar ISIS uku.
-
Bakin Haure Kimani 220 Ne Suka Halaka A Gabar Tekun A Kasar Libya
Jun 22, 2018 12:01Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya ta bada sanarwan halakar bakin haure kimani 220 a gabar tekun a kasar Libya a cikin yan kwanakin da suka gabata.
-
Ana Ci Gaba Da Musayar Wuta A Yankunan Da Suke Dauke Da Rijiyoyin Man Fetur A Libiya
Jun 22, 2018 06:20Kakakin rundunar sojin Libiya ya sanar da cewa: Ana ci gaba da musayar wuta tsakanin sojojin gwamnatin Libiya da gungun 'yan bindiga a yankunan da suke dauke da rijiyoyin man fetur a kasar.