Libiya Ta Yi Barazanar Rufe Iyakarta Da Tunisia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32008-libiya_ta_yi_barazanar_rufe_iyakarta_da_tunisia
Mahukuntan Libiya sun yi barazanar rufe iyakar kasar da Tunisia, muddun dai ci gaba da cin zarafin matafiyan kasar a Tunisia ya ci gaba.
(last modified 2018-08-22T11:32:01+00:00 )
Jun 24, 2018 15:21 UTC
  • Libiya Ta Yi Barazanar Rufe Iyakarta Da Tunisia

Mahukuntan Libiya sun yi barazanar rufe iyakar kasar da Tunisia, muddun dai ci gaba da cin zarafin matafiyan kasar a Tunisia ya ci gaba.

Wata sanarwa da mataimakin fira ministan gwamnatin Libiya dake samun goyan bayan MDD, Ahmad M'etig, ya fitar ta bukaci ministan harkokin wajen kasar da ya dauki duk matakan da suka wajaba na kare lafiyar 'yan kasar ta Libiya a Tunisia.

Haka kuma sanarwar ta bukaci ofishin ministan cikin gida na kasar da ya rufe iyaka da Tunusia, idan gwamnatin kasar ta kasa daukar kwararen matakai akan wadanda ke yi wa huldar dake tsakanin kasashen biyu 'yan uwan juna zagon kasa.

Sanarwar ta ce an dau matakin ne biyo bayan samun bayanai na yadda wasu bata gari ke cin zarafin matafiya 'yan Libiya a yankin Ben Guerdane dake kudu maso gabashin kasar ta Tunisia.

Wasu majiyoyi sun shaidawa kamfanin dilancin labaren Xinhua cewa, jami'an tsaro Libiya na hana wa motocin Tunusia jigilar kayayakin da ake sumogal dinsu musamman na lataroni da kuma abinci, don haka a matsayin maida martani, 'yan Tunisia ke cin zarafin 'yan Libiya dake balaguro a motoci ciki har da hana su komawa kasarsu