Libiya Ta Yi Watsi Da Shawara Turai Kan Tantance Bakin Haure
(last modified Thu, 28 Jun 2018 05:22:51 GMT )
Jun 28, 2018 05:22 UTC
  • Libiya Ta Yi Watsi Da Shawara Turai Kan Tantance Bakin Haure

Kwamitin kare hakkin bil adama a Libiya, ya yi watsi da yunkurin kasashen Turai na kafa sansanonin tantance bakin haure a kasar.

Kwamitin ya ce ya yi watsi da bukatar ce, bisa dalillai na jin kai, tsaro, adalci da dai saurensu musamman idan aka yi la'akari da rikicin da kasar ke ciki.

Kungiyar tarayya Turai dai na son kafa sansanonin tantancewa da kuma bada kariya ga bakin haure tun daga Libiya, inda nan ne mafi akasarin bakin hauren ke yada zango, don duba bukatarsu kafin ba su mafaka a Turai.

Kafin hakan dama Fira ministan Libiya, Fayez Serraj, ya gana da mataimakin shugaban majalisar ministocin Italiya, Mateo Salvini, wanda ya amince bangarorin biyu za su yi wani taro a watan Satumba mai zuwa domin yaki da kwararar bakin haure ba bisa ka'ida ba.