Jun 30, 2018 11:04 UTC
  • Libya: Halifa Haftar Ya YI Gargadi Akan Tura Sojojin Waje Zuwa Yankin Kudancin Kasar

Kamfanin dillancin labarun (AFP) ya ambato kwamandan sojojin Libya Janar Halifa Haftar yana cewa; Fakewa da batun fada da 'yan ci-rani ba zai zama dalilin aikewa da sojojin kasashen waje zuwa kudancin kasar ba

Halifa Haftar dai yana mai da martani ne akan yarjejeniyar da kasashen turai suka cimmawa na samar da wani yanki a wajen turai domin sauke 'yan gudun hijira.
Kasashen turai din suna son kafa cibiyar ne a wata kasa domin karbar 'yan ci-rani wadanda suke fuskantar hatsarin nutsewa a ruwa. Daga wanan cibiyar ne za a tantance 'yan hijirar da basu cancanta ba domin mai da su zuwa kasashen da su ka fito, wadana suka cika sharudda kuma a shigar da su kasashen na turai.

Har ila yau turawan sun amince da su kaucewa barin 'yan gudun hijira suna yawo daga wata kasar turai zuwa wata kasa.

A baya kadan, mataimakin Fira ministan kasar Libya a karkashin gwamnatin hadin kan kasa, ya yi gargadin cewa; Ba za su amince da a kafa sansanin karbar 'yan gudun hijira a cikin kasar ba.

Tags